<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>367</hymn_number>
<title>Allah Ya Kira Shugaba LW367</title>
<lyrics>[V1]
 1) Allah ya kira shugaba
 Na duk mala'ikun sama

[V2]
 Ya ce &quot;Zan aike ka a duniya&quot;
 Ya ce &quot;Na yarda Ubangiji&quot;
 &quot;Ga ni, ka aike ni ko yanzu.&quot;

[V3]
 2) &quot;Ka sabka, ka je duniya&quot;
 Za ka iske budurwa,
 Sunnanta Maryamu ne.&quot;

[V4]
 Mala'ika ya bar gaban Allah,
 Mala'ika ya bar gaban Allah,
 Ya zo, ya iske Maryamu.

[V5]
 3)Ya ce, &quot;Allah ya aiko ni
 Da saƙonsa mafi tsarki
 Shi ne Yesu Ruhunlahi,

[V6]
 Shi za ya shiga mahaifarki,
 Shi za ya shiga mahaifarki
 Shi ne 'Allah tare da mu&quot;.

[V7]
 4) Buduruwa ta razana
 Ta ce, &quot;Ni buduruwa ce
 Ban taɓa shafe namiji ba&quot;.

[V8]
 Mala'ika ya ce, &quot;Gaskiyarki,&quot;
 Mala'ika ya ce, &quot;Gaskiyarki,&quot;
 &quot;Ba ki taɓa shafi miji ba&quot;.

[V9]
 5) &quot;Ai, wannan ikon Allah ne,
 Ni ma, na ji tsoro ƙwarai.
 Da ni da ke, duka ɗaya ne.

[V10]
 Mu bar wannan ga Ubangiji,
 Mu bar wannan ga Ubangiji,&quot;
 In ji Mal'ika Jibra'ilu.

[V11]
 6) Buduruwa ta ɗauki ciki
 Ta wurin Ruhun Mai Tsarki
 Ta haifi Macecin ƴan Adam,

[V12]
 Shi ne Yesu Almasihu,
 Shi ne Yesu Almasihu,
 Shi za ya shirya duniyan nan.</lyrics>
</song>